Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde a ranar Litinin ya kaddamar da kwamitin da zai kula da birnin Ibadan domin lura da aikin kawo karshen ambaliyar ruwa a birnin.
Kwamitin na IUFMP wannan shiri ne na Bankin Duniya da aka kaddamar da zimmar kawo karshen barazanar ambaliyar ruwa a garin Ibadan dake jihar Oyo din.
A yayin kaddamarwar, Gwamna Makinde, ya ce; kowanne memba a kwamitin ana sa ran zai yi amfani da iliminsa basirarsa wajen taimakawa aikin domin kawo karshen barazanar ambaliyar ruwaa da garin Ibadan ke fuskanta.
Gwamnan ya ce kwamitin na IUFMP shi ne kwamitin da ake sa ran zai yi wannan aikin a jihar Oyo.