Gwamna Aminu Bello Masari ya amince da nadin Malam Abdulkadir Bature a matsayin sabon sakataren kungiyar kwallon kafa ta Katsina United
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai mai dauke da sa hannun daraktan wasanni na jihar, Nalado Iro Kankia kuma mai magana da yawun kungiyar Nasiru Gide ya mika wa Kungiyoyin yada labarai.
Nadin na Malam Abdulkadir Bature ya biyo bayan ritayar Malam Sani Tunau ne bayan ya shafe shekaru 35 yana aiki a jihar.
Kafin nadin nasa, Malam Abdulkadir Bature ya kasance tsohon sakataren kungiyar kwallon kafa ta Spotlight wanda a halin yanzu yake rike da mukamin jami’in kula da walwalar kungiyar kwallon kafa ta Katsina United.
Malam Abdulkadir Bature ya kammala karatunsa ne a wata shahararriyar Cibiyar Wasanni ta kasa (NIS) dake Legas, inda ya shafe shekaru 27 yana aiki a fannin wasanni.
A cikin sanarwar, ma’aikatar wasanni da ci gaban al’umma, majalisar wasanni ta jihar katsina da kuma hukumar gudanarwar Katsina United sun godewa sakataren da ya bar aiki tare da yi masa fatan alheri a cikin ayyukansa na gaba.