Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bai wa kungiyar Jamaatu Izalatil Bidah Wa Ikamatul Sunnah, JBWIS gudummawar naira miliyan 100 domin gina Jami’ar Musulunci dake jihar Jigawa.
Kakakin gwamnan, Zailani Bappa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda gwamnan ya bada wannan gudummawar a ranar Litinin a yayin da tawagar shugabancin kungiyar a karkashin Sheikh Bala Lau suka kai masa ziyara a gidan gwamnati.
Gwamna Matawalle ya ce babu gudummawar da za ta yi yawa wajen bunkasa harkokin ilimi, musamman ma ilimin addini.
Inda ya yi kira ga sauran gwamnonin jihohi, da masu hannu da shuni da su tallafawa wannan tunanin, domin a cewarsa kungiyar JIBWIS kungiya ce ta amintattun mutane, da suke son tallafawa al’umma.
Gwamna Matawalle ya bayyana cewa matsalolin rashin tsaro da garkuwa da jama’a da ake samu a yankin arewa wanda ya zama ruwan dare, yana da alaka da rashin son juna da ‘yan arewa ba sa yi. A cewarsa, al’ummar yankin yanzu ba kaunar junansu suke yi ba, shiyasa cikin sauki ake kyankyashe gurbatattu a cikin al’ummar. “Na yi abin da zan yi wajen tabbatar da zaman lafiya a jihata. Zan kuma ci gaba da yi domin kare al’ummata daga gurbatattun mutane.” Ya tabbatar.
Ya kuma shawarci Malamai da su ilmantar da mutane, domin a cewarsa ilimi shi ne ginshikin samar da nagartacciyar al’umma.
Tunda farko, Sheikh Bala Lau ya shaida wa gwamnan cewa tawagarsu sun zo jihar ne domin duba wata makaranta da tsohon gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya bai wa kungiyarsu ta su a garin Shinkafi.