•Mai Mala Buni ya bayyana Gwamna Matawalle a matsayin Shugaban Jam’iyar APC a jihar Zamfara.
• kabin bashi wannan mukamin tsohon Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ne Shugaban Jam’iyar APC a jihar.
• Taron ya sami halar tan, Tsaffin Gwamnonin jihar Zamfara da kuma wasu jiga-jigai daga gwamnatin tarayya, irin su Boss Mustapha da dai sauran su.
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni Kuma Shugaban Kwamitin tsare-tsaren na jam’iyar APC ta kasa, ya bayyana Gwamna Matawalle a matsayin Shugaban jami’iyar APC a jihar Zamfara.
Mr Buni ya bayyana hakan ne a jiya Talata inda ya ce, hakan na daya daga cikin kundin gudanarwar jam’iyar ta APC, na bai wa Matawalle jagorancin jam’iyar a jihar.
Gwamnan na jihar Zamfara ya dai fito Karara a jiya Talata, inda ya bayyana komawar sa, jam’iyar APC daga PDP, a gaggamim taron da ya gudana a garin Gusau.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Sanata daga jihar Zamfara ya bar PDP zuwa APC
Kafin dai komawar Mr Matawalle jam’iyar APC, tsohon Gwamnan jihar Abdulaziz Yari ne Shugaban Jam’iyar a jihar.
Taron dai ya sami halartan tsaffin Gwamnonin jihar, da su ka hadar da: Ahmed Yarina, Mamuda Shinkafi da kuma Abdulaziz Yari.
Ta bangaren gwamnatin tarayya kuwa akwai sakataran gwamnatin Boss Mustapha, Ministan Muhalli Muhammad Mahmoud, da kuma Ministar jinkai Sa’adiya Umar Faruq, da dai sauran su.
Comments 1