Gwamnan Jahar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed a ranar Talata yasha alwashin Gwamnatin sa na tabbatar da gudanar da Sahihin Zaɓe a Jahar A shekarar 2023.
Mohammed ya baiwa jam’iyyun hamayya a Jahar tabbacin cewa zai samar da yanayi mai kyau a garesu domin gudanar da Sahihin zaɓe ba tare da wata matsala ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ka binciki Mutuwar Mahaifina — Kiran Ɗan Gidan MKO Abiola ga Buhari
Ya kuma gargaɗi ƴan siyasa dasu bi dukkanin Dokokin Ƙasar tare da kauce ma duk wani tasgaro daka iya lalata zaman lafiya a jahar.
Gwamnan ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin Mai Martaba Sarkin Bauchi Dr Rilwanu Suleiman Adamu, a lokacin bikin Hawan Daushe da ake gudanar wa bayan anyi Idin Ƙaramar Sallah da kwana ɗaya.
A lokacin da yake bada tabbacin cewa Gwamnatin Jahar shi a ƙarƙashin Mulkin sa zata ba kowa dama a zaɓen, yace babu abinda zai kawo tasgaro ga Jam’iyyun siyasa.
Ya yabawa masu riƙe da Sarautun gargajiya a Jahar da irin goyon baya da haɗin kai ga Gwamnatin sa tun Shekarar 2019.
Tunda Farko a jawabin sa, Mai Martaba Sarkin Bauchi Dr Adamu ya yabawa Gwamna Mohammed da irin girmamawa ga masu riƙe da Sarautun gargajiya, yana mai cewa wannan ba abun mamaki bane ta la’akari da cewa Gwmanan shima Basarake ne.
Comments 1