By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya aika da kudirin dokar hana kiwo a fili na shanu da sauran dabbobi a jihar ga majalisar dokokin jihar Edo (EDHA).
Dokar da aka kafa a wasu jihohin kudancin Najeriya tare da haramta zirga-zirgar shanu da makiyaya ke yi a wuraren taruwar jama’a, wani mataki ne na dakile tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi tsakanin makiyaya da manoma.
Da yake magana kan kudirin dokar yayin zaman majalisar a ranar Talata, kakakin majalisar Marcus Onobun ya ce kudurin ya dade yana karbar bayanai daga mambobi da masu ruwa da tsaki.
Ya kara da cewa an sanya dokar ta baci a nan gaba don ba da damar yin shawarwari daga mambobin majalissar.
A wani labarin makamancin haka, an kuma karanta wani kudiri na kira ga gwamnatin jihar Edo da ma’aikatar ayyuka ta jihar da sauran hukumomin da abin ya shafa da su kamo motoci marasa rajista da babura masu kafa uku a sassan jihar a harabar gidan.
Wanda ya dauki nauyin kudirin, mataimakin mai tsawatarwar majalissar kuma mamba mai wakiltar mazabar Igueben, Ephraim Aluebhosele, ya bukaci majalisar da ta janye kudirin domin karin tuntuba da bayanai daga mambobin da sauran masu ruwa da tsaki.