A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya koka kan yadda ake samun karuwar marayu a jihar.
Ortom ya dora alhakin lamarin a kan zargin mamayewar makiyaya ba tare da kaukautawa ba, yayin da yake jawabi a lokacin bikin godiya ga iyalan Justice Polycarp Kwahar a cocin Evangelical Winning All (ECWA), Ingilishi LCB, dale garin Makurdi babban Birnin jihar.
Gwamnan ya ce a halin yanzu akwai marayu da dama a gidajen marayu da kuma sansanin ‘yan gudun hijira ba tare da sanin yadda zasu kasance a nan gaba ba.
Ortom ya bukaci masu kishin kasa da su tallafa wa marayu da yara marasa galihu kamar yadda ya ce Allah zai girmama irin wannan abin.
Comments 1