By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 na Naira biliyan 155.6 wanda hakan ya sanya yazama doka.
Ortom ya rattaba hannu kan kasafin Kudin ne ranar Juma’a a Makurdi.
Gwamnan ya yi alkawarin bin ka’idojin kasafin kudin tare da aiwatar dasu.
Sai dai gwamnan yace “Ba zan yi wani abu daya wuce tanadin kasafin kudin ba.
“Ko da jihar na bukatar karin kudade za mu tuntubi majalisa don jin dadi ko karin kasafin kudin,” in ji shi.
Kazalika yace aikinsa shi ne aiwatar da dukkan dokokin da majalisar ta zartar ga na baya.