A yau juma’a ce, Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Niger, ya Sanya hannu kan dokar kisan ta hanyar rataya ga duk wanda aka kama da laifin satar Shanu, garkuwa da mutane, ko ta’addacci a daukacin fadin jihar.
Rahotanni sun nuna cewa tun a ranar 1 ga watan Yulin shekarar ne, majalissar dokokin jihar ta amince da Kudirin dokar, na kisan ga masu ba yan bindiga bayanai, masu Garkuwa da mutane, da kuma barayin Shanu.,
Gwamnan ya ce“Garkuwa da mutane da kuma satar Shanu na da hukunci na musamman a kundun tsarin dokar jihar na shekarar 2016, inda aka Sabon ta dokar, domin daukar matakin da ya dace wurin kawar da Yan bindiga” inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC fitar da sunayen Yan takaran na jihar Anambra
Ya kara da cewa, masu bai wa yan bindiga bayanai, wadanda su ne ke tallafa wa masu Garkuwa mutane, su ma zasu fuskaci hukuncin kisa ta hanyar ratayan, kuma a gaban jama’a.
” Yanzu dokar ta Samar da kafar kama duk wani mai garkuwa da mutane, barawon Shanu da kuma mai tamakawa yan bindiga da kayan aiki, ko wani abu makaman cin hakan, na daya daga cikin wadanda dokar kisan ta hanyar ratayan ta shafa” inji shi.
Gwamnan ya ce, an dauki daukan matakin ne, domin ya zama waji bi a magance matsalar tsaro, da ke cigaba da addabar zaman lafiya da kwanciyar hankali jihar, dama kasa baki daya.
Ya kuma nuna damuwar shi kan masu bai wa yan bindiga bayanai, inda ya ce, su na durkusar da dukkannin kokarin hukumomin tsaro, bisa hada kai da masu Garkuwa da mutane da kuma satar Shanu.
.
A karshe Gwamnan ya bayyana kwarin gwuiwar shi, kan cewa, Sanya wa sabuwar dokar hannu, zai taimaka wurin samun hadin kai tsakanin majalissar zartarwar jihar, da kuma majalissar dokokin jihar.
Comments 1