Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya kaddamar da aikin titin Idadu-Agbashi mai tsawon kilomita 24 wanda zai lakume akalla Naira biliyan 3.2.
Yayin da yake kaddamar da aikin gina hanyar a ranar Juma’a a karamar hukumar Doma ta jihar, Sule ya bayyana cewa, an bayar da aikin ne ga Kamafanin Road and Bridge International Nigeria Limited.
Gwamnan ya bayyana cewa tuni ya tanadi kudin da za a yi aikin hanyar kafin a ba da kwangilar.
Ya bayyana cewa kaddamar da titin ya kasance cika alkawarin da ya dauka na gina hanyar a lokacin yakin neman zabesa na shekarar 2019, yana mai cewa alkawarin ya tabbata.
Ya yi alkawarin samar da tsaro ga kamfanin da ke gina hanyar domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci bisa la’akari da wasu bayanai da ake samu.