By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rantsar da sabbin kwamishinoni 14 da majalisar dokokin jihar ta tantance a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jihar.
Da yake jawabi yayin bikin rantsarwar a garin Lafia a ranar Larabar data gabata, Gwamna Sule ya bayyana cewa kwamishinoni goma sha hudu da aka rantsar an zabo su a tsanake daga kananan hukumomin jihar 13 domin samun nagartattun hannaye da za su hada kai da shi wajen kai jihar Nasarawa ga gaci.
Yace, “Yana da muhimmanci a bayyana cewa wannan gwamnati tana mutunta aiki tukuru, tare da sadaukarwa, da aminci da kuma hidimar sadaukar da kai. Ya kamata, duk da haka, in tunatar daku duk kiran da na saba cewa hidimar jama’a amana ce, Don haka, kuna zuwa a mafi tsananin lokacin wannan gwamnati.
“Hakan ya faru ne saboda jama’a na fatan samun ribar dimokuradiyya, kuma gwamnati na cikin zangon karshe na wa’adin mulkinta na farko. Dole ne ku sauke ayyukanku tare da la’akari da ka’idodin mu na yin lissafi, halayya, aminci da kula da dukiyar jama’a cikin hankali”.
A yayin da yake rokon su da su kasance masu gaskiya da rikon amana wajen gudanar da ayyukansu, Gwamnan ya bayyana sunayen kwamishinonin da suka hada da, Yakubu Kwanta daga karamar hukumar Akwanga, Yusuf Turaki daga karamar hukumar Awe, Aishatu Ibrahim daga karamar hukumar Awe, Salihu Enah daga karamar hukumar Doma, Umar Gurku. daga karamar hukumar Karu.
Sauran su ne; Hannatu Abimiku daga karamar hukumar Lafia, Nuhu Oshafu daga karamar hukumar Keana, Idris Mohammed-Idris daga karamar hukumar Keffi, Mohammed Sarki daga karamar hukumar Lafiya, Fatu Sabo daga karamar hukumar Nasarawa, Yakubu Lawal daga karamar hukumar Nassarawa Eggon, Daniel Agyeno daga karamar hukumar Obi, Ahmed Baba-Yahaya daga karamar hukumar Toto da kuma Lucky Yargwa daga karamar hukumar Wamba.
Sannan ya yabawa shugaban majalisar da ‘yan majalisar jiha bisa yadda suka hanzarta tantancewa da tabbatar da wadanda aka nada a matsayin kwamishinoni tare da yin alkawarin ci gaba da hada kai da bangaren majalisar dokoki domin tabbatar da ci gaban jihar cikin sauri.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, tun da farko majalisar dokokin jihar ta cire sunan kwamishinan na goma sha biyar, Abdulkarim Kana, wanda shi ne babban lauya kuma kwamishinan shari’a, saboda nadin da ya yi daga majalisar ministocin data gabata ya ci gaba da aiki saboda ba ya cikin wadanda gwamnan ya kora.