Gwamnan Jihr Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC mai mulki a kasar nan tana gab da rugujewa ta inda PDP za ta karbi mulki cikin sauki kana ta fitar da al’umma daga kunci da take ciki.
Gwamna Tambuwal ya ayyana hakan ne a garin Gwadabawa Shelkwatar Karamar hukumar Gwadabawa yayin tarbar wasu yayan jam’iyyar APC kimanin dubu goma sha biiiyu da suka yi hijira zuwa PDP.
Ya ce tuni yan Najeriya suka dawo daga rakiyar APC sakamakon abin kunya da ta yi rashin cika alkawrua da ta daukar wa yan kasa.
Bugu da kari ya ce a halin da ake ciki ko tsinke APC ba za ta iya dagawa ta nuna ba na abin alkairi da ta yi don haka ya ce babu wanda ke tare da ita a jihar.