By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnan jihar Imo, Sen. Hope Uzodimma ya nuna alhinin sa bisa rasuwar tsohon shugaban riko na Najeriya, Cif Ernest Shonekan.
Gwamnan, wanda a safiyar yau, ya umarci jami’an gidan gwamnatin jihar Imo, da ma dukkan ofisoshin gwamnatin jihar da ayi kasa-kasa da tutoci, sannan ya bayyana Cif Ernest Shonekan a matsayin mutum mai gaskiya wanda ya jajirce ya tsaya cak a lokacin hatsari, amma duk a wani yunkuri na kare hadin kan Najeriya.
Cif Ernest Adegunle Oladeinde Shonekan GCFR, haifaffen jihar Ogun, lauyan Najeriya ne wanda ya rike mukamin shugaban kasa na rikon kwarya daga 26 ga watan Agusta 1993 zuwa 17 ga Nuwamba 1993. An yi masa lakabi da Abese na Egbaland daga shekarar 1981.
Ya kasance yana da shekaru 85 kuma ya yi rayuwa mai gamsarwa.
Za a tuna da shi a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga hidimar ƙasar kuma uban kasa.