Rahotanni dake fitowa da yammacin nan, na nuni da cewa gwaman Kogi Yahaya Bello kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar ya lashe mazabarsa, inda ya doke abokan hamayyarsa na PDP, Musa Wada da Natasha Akpoti na SDP.
Mazabar ta sa dake gundumar Okene-Eba/Agassa/Ahache mai lamba, dake karamar hukumar Okene, a jihar Kogi, ya samu kuri’a 716.