A wani mataki na gani ta kawo karshe tirka-tirkarta ta cikon gida, Jam’iyyar APC mai mulki a kasar nan ya naɗa Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello a matsayin shugaban kwamitin da zai sasanta yayanta da suka nuna tawaye a birnin tarayya Abuja.
Wannan nadi na zuwa nw yan kwanaki gabannin babban zaben fitar da gwani na kananan hukumomin birnin tarayya Abuja da jam’iyyar za ta yi.
Cikin takardar nadin da Sakataren tsare-tsaren gudanar da babban taron Jam’iyyar Sanata John Akpan ya fitar, ta ce daga cikin karin mutane da za su shiga sasantawar akwai Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sulea matsayin mamba da kuma Honorabul Olaide Akinremi da zai kasance sakataren kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Sanata Ahmad Yusuf Yusuf da Dakta James Lalu sai Honorabul Cletus Dick gami da Honorabul Uche Ogah.
Ana sa ran kwamitin na Yahaya Bello zai yi zaman sasantawar ne bisa doka da tanadin da Kundin Jam’iyyar ya yi.