Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya nada Sanata Hassan Mohammed Nasiha Gusau a matsayin mataimakin gwamna, bayan tsige Barista. Mahdi Aliyu Gusau.
Kafin nadin nasa, Hassan Nasiha ya kasance Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya a Majalisar Dattawa.
A halin da ake ciki yanzu haka, tuni majalisar dokokin jihar a zamanta da ta koma a yau Laraba ta tsige Barista Mahdi Aliyu Muhammad Gusau a matsayin mataimakin gwamnan jihar ba tare da bata lokaci ba.
A cikin wata sanarwa da kakakin majalisar, Mustafa Jafaru Kaura ya fitar, ya ce an samu tsohon mataimakin gwamnan da dukkan zarge-zargen da ake yi masa.