Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya amince da a gina sabuwar babbar makarantar Sakandare a garin Pulka dake karamar hukumar Gwoza a jihar.
Gwamna Zulum ya amince da hakan ne a ranar Juma’a a yayin da yake gabatar da jawabi ga dubban ‘yan gudun hijira da al’ummar garin na Pulka.
Kafin ya bar garin na Maiduguri zuwa Pulka, sai da gwamnan ya sanya aka dibi abinci a motocin Tirela wanda aka rabawa al’ummar na garin Pulka wanda gwamnan ya sanya ido a yayin rabawa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa sama da mutum dubu ashirin ne wanda ya hada da al’ummar garin Pulka da ‘ya gudun hijira suka amfana da wannan tallafin abincin.