Gwamna Babagana Zulum na Borno a ranar Lahadin da ta gabata ya saki Naira miliyan 100 da kayan aikin karfafawa masu dinki 5,340 don inganta sana’o’insu.
Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata, a dakin taro na gidan gwamnati dake Maiduguri.
KARANTA WANNAN LABARIN: APC Ta Dakatar Da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Na Kasa A Yankin Arewa Maso Gabas
Ya ce: “Mun raba Naira miliyan 100 ta hannun Bankin Renonasance Microfinance ga masu sana’ar dinki 2,000 tare da wasu 3,340 da ke karbar nau’ukan kayan aikin da suka hada da injinan masana’antu, injin keken dinki, da injinan samar da wutar lantarki da dai sauransu.
“Za mu so sauran kungiyoyin masu sana’ar dinki su hada jerin sunayen mambobi daga dukkan kananan hukumomi 27 da ba su ci gajiyar rabon kayan yau ba, domin mu tallafa musu a atisayen da muka yi karo na 2 da na 3,” in ji Zulum.
Tun da farko, Manajan Darakta na Bankin Renaissance Microfinance, Dokta Bello Ibrahim ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su yi amfani da damar wajen amfani da su.
Taron ya samu halartar shugaban jam’iyyar APC na Borno, Alhaji Ali Dalori, da dan takarar jam’iyyar a zaben Sanatan Borno ta tsakiya, Mista Kaka Lawan, wadanda dukkansu sun goyi bayan Gwamna Zulum yayin gabatar da mutane 5,340 da suka ci gajiyar shirin.
Zulum ya sanar da cewa matakin na ranar Lahadi shi ne karon farko yayin da za a tallafa wa karin kungiyoyin masu dinki daga fadin kananan hukumomi 27.
Malam Ibrahim Kachalla, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin a karkashin kungiyar Amalgamated Tailoring Association, ya yabawa gwamnan bisa wannan tallafin, inda ya ce hakan zai ci gaba da bunkasa sana’o’insu.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa masu dinki 2,000 sun karbi Naira 50,000 kowannensu yayin da wasu 2,000 suka samu injin keken dinki.
Wani rukuni na 200 sun sami injinan masana’antu, 40 sun karɓi injunan sakawa, yayin da 100 suka sami injinan samar da wutar lantarki. (NAN)
A wani labarin kuma, Gwamnatin Zamfara Ta Dauki Jami’an Yaki Da ‘Yan Daba 2,500
Gwamnatin Zamfara ta horar da hukumar yaki da ‘yan daba a jihar da sabbin ma’aikata 2,500 da aka dauka domin su taimaka wajen yaki da ‘yan fashin siyasa, shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran laifuka masu alaka da su a jihar.
Da yake yiwa manema labarai jawabi a Gusau babban birnin jihar, kwamandan hukumar Hon. Bello Bakyasuwa ya ce: “Babu shakka ayyukan Hukumar suna samun nasara; ɗaukar makamai, ƴan daba na siyasa, shan muggan kwayoyi da fashi da makami sun ragu sosai.”