Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis a Maiduguri, ya bayyana cewa gwamnati ta ware gidaje 259 tare da sakin Naira miliyan 110 ga rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar.
Zulum ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bankin ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Borno (NPFM Bank).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yada labarai Malam Isa Gusau ya fitar a ranar Juma’a.
Solacebase ta ruwaito cewa an tsara bankin Microfinance ne don samar da ayyukan kudi don tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i ga iyalan ‘yan sanda da ‘yan uwansu da fararen hula a jihar Borno.
Sanarwar ta ce bikin kaddamar da bankin a Maiduguri ya samu halartar babban sufeton ‘yan sanda, Usman Baba Alkali.
“Kafin kaddamar da shirin, Zulum ya bayyana cewa rabon gidaje sama da 259 ga ‘yan sanda an yi shi ne domin biyan diyya ga hukumar a jihar kan yadda gwamnati ta yi amfani da wasu kaso na ‘yan sanda, domin bunkasa wasu kayayyakin more rayuwa a babban birnin jihar.” Sanarwar ta ce.
‘’Akan Naira miliyan 110 da ya bayyana, gwamnan ya ce kashi 50% na kudin, wanda ya kai miliyan 55, gudunmawar Borno ce ta hannun jari da nufin bunkasa ayyukan bankin a matakin farko.
“Sauran kudin miliyan 55, Zulum ya ci gaba da bayyana cewa, za a yi amfani da shi wajen tallafa wa iyalan jami’an ‘yan sanda ta hanyoyi biyu.
“Na farko, Zulumya ce, ayi amfani da Naira miliyan 25 a rabawa iyalan ‘yan sandan da suka mutu a bakin aiki.
‘’Ya ba da umarnin a ajiye kudaden a asusun ajiyar yaran da ‘yan sandan da suka mutu suka bari.
‘’Bayan Naira miliyan 30, inji gwamnan, za a saka shi a asusun ajiyar kudi domin tallafa wa mata ‘yan sanda da ke aiki a fadin jihar Borno.
Zulum ya yabawa babban sufetan yan sandan kasar nan IGP Alkali bisa kaddamar da reshen bankin na Borno wanda ya ce, ya nuna yadda IGP ya ba da fifiko ga jin dadin ‘yan sanda.
‘’Gwamnan tare da IGP, da shugabannin bankin da wasu manyan jami’an ‘yan sanda, sun kaddamar da reshen ne ta hanyar yankan kaset.
A cewar sanarwar da ke gaban hukumar, Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya bayyana goyon bayan da Gwamna Zulum ke baiwa rundunar ‘yan sandan Najeriya a matsayin mai girma.
“Mai girma gwamna, muna so mu gode maka bisa irin dabaru da rundunar jihar ke samu na yin aiki yadda ya kamata wajen yakar miyagun laifuka. Ina sane da cewa Jiha daya tilo da ta samu motocin yaki guda shida tare da mika su ga ‘yan sanda ita ce Jihar Borno. Muna so mu gode muku da gaske da kuka dauki mana wahalarmu, da kuka yi mana alheri, da kuka yi mana karamci, da kuka zo wajen taimakonmu ta fuskar samar da walwala da kayan aiki,” in ji IGP.
”IGP din ya samu rakiyar shugaban hukumar kula da kananan kudi ta bankin, Azubuko Joel Udah, da manajan darakta na bankin, Mista Akin Lawal da manyan ‘yan sanda yayin da Zulum ya tafi tare da sakataren gwamnatin jihar Borno, Usman Jidda Shuwa, da wasu. mambobin majalisar zartarwa ta jihar Borno.”