By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da ayyuka 22, galibinsu makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya a shiyyar dake kudancin jihar.
Zulum ya isa Biryel, hedkwatar karamar hukumar Bayo a ranar Talata da yamma kuma ya wuce can kafin kaddamar da ayyuka a Bayo ranar Laraba.
Mai magana da yawun gwamnan, Malam Isa Gusau a cikin wata sanarwa, yace Zulum ya kaddamar da ayyuka 22 daga cikin sauran ayyuka da dama da gwamnatin ta aiwatar a kudancin Borno.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gusau ya bayyana cewa ayyuka 22 sun hada da sabbin makarantun sakandire da firamare guda 13 wadanda aka gyara su, Cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko guda shida da gine-ginen kananan hukumomi uku da suka hada da ofisoshin ‘yan sanda biyu da gidan gwamnati da kuma rukunin shaguna.
Sanarwar ta bayyana cewa, an kafa ayyukan guda 22 a kauyuka da garuruwan kananan hukumomin Hawul, Shani, Bayo da kwaya kausar a kudan cin Borno.
Gusau ya bayyana cewa wasu daga cikin makarantun da Zulum ya kaddamar sun hada da sabuwar makarantar gwamnati mai girman ajujuwa 30, da kuma watar makarantar sakandare ta gwamnati mai ajujuwa 20, makarantar sakandaren al’umma mai azuzuwa 20, makarantar firamare mai ajujuwa 20 daga cikin su. wasu.
Kakakin ya tunatar da cewa, a cikin shekaru biyun da ya yi, Zulum ya aiwatar da manyan ayyuka 556 wadanda a yanzu an zarce su daga ranar 29 ga Mayu, 2021 zuwa yau.
Haka kuma ana sa ran gwamnan zai duba manyan gidajen da aka kammala kuma aka ware wa wasu hakimai da masu unguwanni.
A matsayin wani muhimmin bangare na tafiyar tasa, Gwamna Zulum ya tattauna da shugabannin rundunonin soji da na sa kai a wani bangare na hanyoyin da ya saba bi don gano bukatu na gaggawa da kuma karfafa matakan tsaro a yankunan kudancin Borno.