Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya tsige shugaban ma’aikatan jihar, Mohammed Hassan. Sanarwar tsigewar ta fito ne daga bakin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Shuwa wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Maiduguri.
Shuwa ya tabbatar da cewa gwamnan ya amince da nadin Simon Malgwi a matsayin sabon shugaban ma’aikatan jihar, wanda nadin na shi zan fara aiki nan take.
Gwamna Zulum ya ce an tsige Mohammed Hassan a matsayin shugaban ma’aikatan jihar nan take, tare da tabbatar da Barista Simon Malgwi a matsayin sabon shugaban ma’aikatan wanda shima aikinsa zai fara nan take.
Shuwa ya tabbatar da cewa kafin nadin Malgwi a matsayin shugaban ma’aikatan, shi ke rike da mukamin Sakataren ma’aikatar ilimi kuma babban mai ba da shawara ta fuskacin shari’a.