Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya raba kayan abinci da tsabar kuɗi ga gidaje 100,000 na marasa galihu a cikin babban birnin Maiduguri da Ƙaramar Hukumar Jere.
Da yake jawabi a wajen taron rabon a Maiduguri a jiya Talata, Zulum ya ce matakin wani ɓangare ne na rabon kayan agajin da gwamnati ke yi don rage wahalhalun da tashe-tashen hankula da annobar COVID-19 ta haifar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan magance Matsalolin da Shugabannin Ƙasar nan su ka kasa magance wa — Tinubu
A cewar Zulum, gwamnati ta yi bincike na tsanaki waje zaɓo waɗanda su ka ci gajiyar shirin adomin tallafa musu, musamman a wannan lokaci na azumin Ramadan.
Ya ce an kuma miƙa makamancin tallafin ga mabuƙata a sauran ƙananan hukumomin.
Zulum ya ce duk mazajen da su ka ci gajiyar tallafin za su samu buhun shinkafa kowanne, yayin da mata za su samu N10,000, da kuma kilo 5 na sukari kowannen su.
A nasa sakon fatan alheri, shugaban Ƙaramar Hukumar Maiduguri, Alhaji Bolori, ya bayyana matakin a matsayin wanda ya dace, inda ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su rama kyautar da a ka yi musu ta hanyar amfani da lokacin Ramadan wajen yi wa jihar da kasa baki daya addu’ar zaman lafiya.