Gwamnatin jihar Borno ta ce ta ware asusu na musamman don habbaka bincike da nazari kan abin dake haifar da yawaitar ciwon koda a jihar.
Isa Gusau, mai bai wa Gwamna Babagana Zulum shawara kan harkokin watsa labarai ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Maiduguri.
Gusau ya ce jihar ta gayyaci kwararrun manazarta su kawo mukalolinsu kan dalilan da suke jawo cutar.
Ya kara da cewa, gwamnatin za ta bada kudade ga masu binciken wanda ake burin mayar da hankali kan ruwa, muhalli da sauran abubuwan da suke jawo cutar.
A cewarsa, gwamnatin ta dauki matakin ne domin rage yaduwar ciwon kodan da ake a jihar.