Wakilinmu Bashir Dan Borno
Zababben Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya Kai wata Ziyarar Ba zata a Asibitin Umaru Shehu Ultra Modern, inda ya tarar da Tarin Majinyata ba tare da Likitoci ba Balle a Basu Magani.
Kazalika Rahoton ya ce Gwamnan Ya sa an rika kiran Likitocin ta waya amma da yawa daga cikin su ba su daga wayar ba, kadan ne daga cikin su suka ji wa ya Kira inda suka rika zuwa asibitin a guje.
Wakilin Jaridar Dimokuradiyya, ya tabbatar Mana cewa cikin Malaman Asibiti 138 da ya kamata su zama a Bakin aiki Mutane 10 ne kacal Gwamnan ya samu a Bakin aiki.