Gwamnan Jihar Adama Amadu Fintiri ya sanya ma’aikatan wucin gadin gidan gwamnatin Jihar cikin farin ciki da annuri, bayan da ya basu aiki na dindindin.
Kazalika gwamnan ya ce zai kuma zaɓi Babban Jami’in Kula da Gidan Gwamnatin wanda zai rika ka da walwala da jin daɗin ma’aikata.
Gwamnam ya sanar da haka ne a jiya bayan da ya karbi bakwancin yan jaridu da kananan ma’aikatan gidan gwamnati a wata liyafar buɗa baki da ya shirya musu a gidan Gwamnatin dake Yola Fadar Gwamnatin Jihar.
Fintiri ya ce bisa lura da kokari da irin jajircewar su ne ya ga ya dace ya musu wannan Alkhairi, a matsayin goron Sallar su.
Ya kuma bukace su da su ci gana da sanya kasarnan cikin addu’o’in su bisa ganin irin halin niyasu da take ciki musamman a bangaren tsaro.
Bugu da kari ya ce gwamnatin na matukar damuwa da yanayin halin al’umma, shi ya sa ne yake ci gaba da tallafa musu don daukaka Jihar.
Daga bisani kuma Fintiri ya mika kokon bararsa ga Ma’aikatan da su hada karfi da karfe don cimma muradun da ya sa a gaba na ginin al’umma ta hanyar aikace-aikace raya kasa.
Ma’aikatan na gidan gwamnati a nasu bangare sun jinjina qa kokarin gwamnan, inda suk ce tunda suke babu wanda ya taɓa yi musu wannan karamci