Gwamna Aminu Masari, a ranar Talata, ya umarci jami’an tsaro a jihar Katsina da su tabbatar da kubutar da mabiya addinin Kirista da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su ranar Lahadi.
An bayar da umarnin ne a wata ganawa ta musamman da gwamnan ya yi da shugabannin hukumomin tsaro daban-daban a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Ni Da Masaniyar Simamen Da Aka Kai Gidan Emefiele – Kakakin ‘Yan Sanda
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin a karfafa tsaro a dukkanin wuraren ibada da ke jihar da nufin tabbatar da tsaron lafiyar masu ibada a wuraren.
Sanarwar da Babban Daraktan Gwamna Masari mai kula da sabbin kafafen yada labarai, Al-Amin Isah, ya fitar a yammacin ranar Talata bayan taron na kunshe da umarnin.
Gwamnati ta ce adadin mutanen da aka sace sun kai 8 wadanda aka bayyana sunayensu kamar haka Rabi Isiyaku, Rabi Saidu, Saratu Hadi, Nusaibu Shuaibu, Gaje Adamu, Bilikisu Tijjani, Iliya Tijjani da Aisha Tijjani.
Sanarwar ta kara da cewa Gwamna Masari “ya bukaci jami’an tsaro da su yi duk mai yiwuwa don ganin an ceto wadanda lamarin ya shafa tare da tabbatar da cewa sun sake haduwa da iyalansu.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa gwamna Masari ya umurci sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma a jihar da su baiwa jami’an tsaro bayanai na gaskiya kan masu aikata laifuka a yankunansu daban-daban.
Sanarwar ta kuma baiwa mazauna jihar tabbacin gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba, ta kuma kara da cewa gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro sun dauki sabbin matakai na tabbatar da tsaron lafiyarsu.
A wani labarin kuma,Buhari: An Kashe Dala Biliyan 1 Don Kwato Yankunan Dake Hannun ‘Yan Ta’adda
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata ya ce Najeriya ta kwato yankuna daga hannun ‘yan ta’adda ta hanyar zuba jarin sama da dala biliyan 1 don samun makamai masu linzami daga Amurka da sauran kasashen abokan hulda domin ci gaba da ayyukan yaki da ta’addanci tun shekarar 2015.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi
a wajen taron zaman lafiya na Afirka, 2023, a Nouakchott, Jamhuriyar Musulunci ta Mauritania.