Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya kaddamar da wani kamfanin sarrafa shinkafa na biliyoyin naira mai suna Gerawa Rice Mills LTD mai karfin nika ton 560 na shinkafa Paddy a kowace rana a Kano.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa Emefiele ya ce kafa kamfanin shinkafa na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na karkata tattalin arzikin Najeriya zuwa Noma.
Da yake jawabi a wajen taron a ranar Talata, Emefiele ya bayyana fatansa na cewa kamfanin shinkafa zai inganta samar da abinci a kasar.
A cewarsa, Gwamnatin Tarayya za ta cigaba da tallafawa manoma ta hanyar shirinta na Anchor Borrowers Scheme a fadin kasar nan, kamar yadda ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa kamfanin Gerawa Mills Nigeria Limited idan bukatar hakan ta taso.
“Wannan wani bangare ne na kokarin Gwamnatin Tarayya na habaka tattalin arzikinmu. Kamfanin Gerawa Rice Mills LTD zai inganta samar da abinci a kasar.
“A namu bangaren, za mu ci gaba da zama Manoma ta hanyar shirin mu na Anchor Borrowers Scheme. Gwamnatin Tarayya za ta kuma tallafa wa rukunin kamfanonin Gerawa a duk lokacin da bukatar hakan ta taso”.
Shima da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin noman shinkafa a hukumance, gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana ci gaban da aka samu a matsayin mai yawa, inda ya kara da cewa sabon kamfanin shinkafar da aka kaddamar zai samar da ayyukan yi ga mazauna jihar.
Ganduje ya kuma jaddada cewa wannan ci gaban ya zo ne a sakamakon manufofin gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kamar yadda ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya na karkata akalar tattalin arziki.
“Wannan babban ci gaba ne, wadannan nasarorin za su samar da guraben aikin yi ga matasan mu na hadin gwiwa.
”Wannan abu ne mai yiwuwa a gwamnatin Shugaba Buhari. Don haka, ina son in yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa yadda ta karkata akalar tattalin arzikin kasa,” inji shi.
Da yake karin haske kan aikin noman shinkafa na biliyoyin naira, shugaban rukunin kamfanonin Gerawa, Alhaji Isa Muhammed Gerawa ya ce an kashe naira biliyan 15 wajen kafa kamfanin.
A cewarsa, kafa kamfanin an yi shi ne da nufin kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa Najeriya a matsayin kasa ta samu isasshen abinci.
Alhaji Gerawa ya ce kamfanin noman shinkafa zai samar da ayyukan yi ga matasa kusan 20,000 a jihar Kano.
“An kashe naira biliyan 15 wajen kafa kamfanin kuma an dauki matakin ne domin cika alkawarin gwamnatin tarayya na tabbatar da wadatar abinci.
“Muna fatan za a samar da ayyukan yi ga matasa dubu 20”.