Gwamnan jihar Bauchi, Lauya Muhammad A. Abubakar na jam’iyyyar APC, da sabon Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Bauchi, CP Habu Sani Ahmadu sun sha alwashin shawo kan matsaloli da kalubalen tsaro da jihar Bauchi ta ke fuskanta. Sun sha wannan alwashin a tsakaninsu ne a lokacin da kwamishinan ‘yan sandan ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar ga gwamna Abubakar a ranar Lahadi. Da ya ke jawabinsa, CP Ahmadu ya shaida cewar tunin ya gana da dukkanin Kwamandojin yanki-yanki da sauran manyan jami’an da suke karkashin shalkwatarsa domin ganin yadda za a yi a inganta tsaro da shawo kan dukkanin matsalolin tsaro da suke fuskantar jihar ta Bauchi. Kamar yadda ya ke shaidawa, cewar jami’an tsaro na ‘yan sanda a jihar sun sake nazarin sabbin daburun aiki da tsare-tsaren daukan matakan da zai basu cikakken damar cin nasarar da suka sanya a gaba. Kwamishinan ya kuma jinjina wa gwamnan jihar Abubakar a bisa hadin kai da goyon bayan da yake baiwa ‘yan sanda a jihar domin su samu zarafin sauke nauyin da ke kansu. Daga bisani ya nemi gwamnatin ta ci gaba da basu cikakken hadin kai domin su samu nasarar gudanar da aiyukan su yadda ya dace. Kwamishina ‘yan sandan ya baiwa masu zuba jari a jihar musamman ganin cewar yanzu haka aikin hadakar Mai na gudana a jihar tabbacin cewar zaman lafiya da tsaro mai nagarta. Da ya ke maida jawabinsa, gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar ya yi wa sabon Kwamishinan lale da marhaban zuwa jihar, yana mai cewa jihar tana cin gajiyar zaman lafiya mai tsafta a dukkanin fadin jihohin arewa maso gabas, inda ya nuna jihar a matsayin jihar da ta fi kowace jiha samun zaman lafiya a yankin. Ya kuma ce jihar tana ci gaba da morar wannan zaman lafiyar wanda tun lokacin da ya hau kan mulki babu wani rikicin da aka samu aukuwarsa a jihar. Daga bisani ya kirayi ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da su kara ninka hazakarsu wajen shawo kan ‘yan matsalolin tsaro da suke fuskantar jihar a halin yanzu. “Ina son ku tashi tsaye wajen shawo kan matsalar ’yan Sara-Suka wadanda a sakamakon su an samu asarar dukiyoyin jama’a da dama. Za mu tabbatar da yin duk mai iyuwa wajen ganin an shawo kan wannan matsalar,” Inji gwamnan jihar ta Bauchi.