Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a ranar Litinin ya amince da nadin Nuhu Ahmed Wabi, a matsayin sabon Sarkin Jama’are.
Wabi, wanda daya ne daga cikin ‘ya’yan marigayi Sarki, an nada shi ne bayan rasuwar mahaifinsa, Ahmadu Muhammadu Wabi III, wanda ya shafe shekaru 50 a kan karagar mulki a ranar Lahadi, 6 ga Fabrairu, 2020.
Da yake sanar da nadin sabon sarkin a ranar Litinin a garin Jama’are, Gwamna Mohammed ya ce nadin Nuhu Ahmed Wabi ya biyo bayan “nazari sosai kan sunayen da amintattun masarautar Jama’are suka ba da shawara akan su”.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jihar (SSG), Ibrahim Kashim, yayi kira ga sabon sarkin da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa na kula da talakawansa ba tare da wani fifiko a tsakanin su ba.
Yayin da yake baiwa sabon sarkin aikin, ya Kuma ja hankalina da ya yi koyi da kyawawan halaye na jagoranci irin na mahaifinsa marigayi, Gwamna Mohammed ya bayyana cewa sabon uban gidan sarauta ya kasance mafi kyawun abin koyi a cikin mahaifinsa marigayi, wanda ya yi rayuwa mai kyau da ta dace a yi koyi da ita.
Daga nan gwamnan ya kuma taya Nuhu Ahmed Wabi murnar nadin da aka yi masa tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya da wadata.
DAILY POST ta rahoto cewa kafin nada shi a matsayin sabon Sarkin Jama’are, Nuhu Ahmed Wabi, shi ne Yarima mai jiran gadon sarautar Jama’are.
Kazalika Kuma Shi ne babban dan marigayi sarkin na garin Jama’are.