Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya umurci ma’aikatar ilimi ta jihar da hukumar kula da bayar da tallafin karatu ta jihar da su hada kai don biyan kudin tallafin karatu.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a lokacin da ya karbi zababbun jami’ai da mambobin kungiyar daliban jihar Bauchi ta kasa a gidan gwamnati da ke Bauchi.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko kan jin dadin dalibai da samar da ingantaccen ilimi a jihar.
Mohammed ya kuma umarci ma’aikatar da hukumar da su fito da sahihan dalibai ‘yan asalin jihar, da ke karatu a cibiyoyi daban-daban a fadin kasar nan kafin a raba kudaden.
Gwamnan wanda ya yabawa daliban kan zaben da suka yi cikin kwanciyar hankali, ya kuma gargade su da su guji shiga duk wata haramtacciyar hanya da za ta kawo cikas ga makomarsu.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban kungiyar na kasa, Mahmud Abubakar, ya bukaci gwamnan da ya kara saka hannun jari wajen farfado da ilimi a Bauchi.