Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nada dan Sheikh Dahiru Usman Bauchi, Dakta Abubakar Sirinbai Dahiru Bauchi a matsayin sabon shugaban hukumar ilimi ta bai daya ta jihar Bauchi, wato Bauchi SUBEB, kamar yadda jaridar Blue Print ta tabbatar.
Shi dai Dahiru Bauchi fitaccen Malamin addinin Musulunci ne dan asalin jihar Bauchi, amma mazaunin garin Kaduna da ya dade yana yi ma Musulunci hidima, kuma jagora ne a tafiyar darikar Tijjaniyya.
Nadin ya fito ne a sanarwar da ofishin Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Sabiu Mohammed Baba ta bayyana, inda sanarwar ta kara da cewa gwamnan ya nada Alhaji Yakubu Barau Ningi tare da Zakari Ibrahim Muhammad a matsayin kwamishinoni a kwamitin gudanarwa ta hukumar.
Sauran membobin wannan kwamiti sun hada da Yusuf Abdullahi Itas, Abbas Waziri da Comfort Audu, kamar yadda gwamnan ya nada su, daga karshe sanarwar ta kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.