Gwamnatin jihar Borno ta ce za ta gina gidaje 1,100 a wadansu kauyuka guda biyu wanda ya hada da Ngoshe da Warabe da mayakan Boko Haram suka lalata a cikin karamar hukumar Gwoza.
Gwamna Babagana Zulum ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyara garin Limankara da kuma Gwoza.
Gwamnan a yayin ziyarar, ya karbi shawarwari daga shuwagabannin garuruwan biyu domin bayyana masa hakikanin wurin da za a gina gidaje 550 a kowanne kauye guda biyun.