Gwamna David Umahi na Ebonyi ya bayyana aniyarsa ta nada mutum 800 a matsayin mashawarta kari akan mutum dubu 4 da yake da su a karkashin gwamnatinsa.
Umahi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Abakaliki a yayin da yake ganawa da membobin zartarwa na jihar, da kuma ‘yan majalisa tare da shugabannin kananan hukumomin da sabbin masu mukamin da sauran masu ruwa da tsaki.
Duk da nadin mutum 185 da ya yi kwanan nan a matakan EAs da STAs da kuma TAs, ya sake nada mutum 200 masu irin mukamin nan. Ya ce gab suke da su samar da masu mukaman EAs, STAs da TAs guda 800 a karshen wannan zaman da suke gudanarwa. Ya ce kuma za su ba da mukaman ne daga kowacce gudummawa.
Ya tabbatar da cewa masu mukamai a matakin EAs za a rika ba su naira 150,000, inda zai zama dubu 100,000 a matsayin albashi sauran dubu 50 a matsayin na sauran zirga-zirga. Masu mukaman STAs za a rika ba su Naira 120,000 sai masu mukaman TAs za a rika ba su dubu 100.