Gwamnan Gombe Ya Kafa Kwamitin Binciken Musabbabin Rikicin Billiri
Daga Sulaiman Musa
Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kafa tare da kaddamar da kwamitin bincike na musamman domin gano musabbabin rikicin da ya auku a karamar hukumar Billiri wanda ya barke tsakanin ranakun 17 zuwa 20 ga Fabrairu 2021 kan nadin sabon Mai Tangle.
A wani sanarwar da Isma’ila Uba Misalli, Daraktan yada labaran gwamnan ya fitar da yammacin nan ya lura da cewa Kwamitin an kafa ne domin zakulowa da gano hakikanin dalilan da suka jawo wannan rikicin.
Da yake gabatar da jawabinsa a wajen bikin kaddamarwar da mambobin Kwamitin, Gwamnan ya ce an kafa kwamitin binciken ne bayan mummunar zanga-zangar da ta yi sanadin mutuwar wadanda ba-su-ji-ba-su-gani ba, da lalata dukiya mai tarin yawa da suka hada da gidaje, wuraren kasuwanci da Masallatai, cocina wanda hakan ya haifar da gudun hijirar mutane da dama.
Ya ce zanga-zangar ta barke tun kafin gwamnati ta yanke hukunci kan wanda za ta nada amma ya jaddada cewa wani abin da ba za a iya musantawa ba shi ne, yada labaran karya ya ba da gudummawa matuka a kan karuwar tashin hankalin.
Ya ce saboda wannan ne ya sa gwamnatin jihar Gombe ta yi amannar cewa ana bukatar gano musabbabin rikicin domin hukunta wadanda ke da hannu da kuma daukar matakan da suka dace don hana afkuwar hakan a nan gaba.
Gwamna Yahaya ya bukaci mambobin kwamitin da su kasance masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da aka daura musu tare da yin kira ga mutane da su taimaka wa kwamitin da bayanai na gaskiya, masu amfani da gaske.
Ya kara da cewa kwamitin binciken ya kunshi mutane masu halin kirki wadanda aka zakulo daga kwararru daban-daban tare da Mai ritaya Mahmud Gurama a matsayin Shugaba.
Membobin sun hada da: AIG mai ritaya na ‘yan sanda Zubairu Mu’azu, Barr Mahmud Bappa Aliyu, Sharon Faliya Cham da Rev Bitrus Urbanus Thaba.
Sauran sun hada da: Abdulhamid Salisu Bello, Victoria Mamuda Usman, Barr Robert Wabida a matsayin Memba, Abdullahi Jalo (Castic), Dr Ya’u Ahmed Kashere yayin da Barr Musa Sa’idu Sakatare da HN Nwoye ESQ za su yi aiki a matsayin Sakatare da Lauya a Hukumar.