- Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya amince da nadin babban sakataren yada labaran sa.
- Sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa.
- Sabbin nade naden sun fara aiki nan take
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Hamisu Muhammad Gumel a matsayin babban sakataren yada labarai da sauran masu taimaka wa harkokin yada labarai,Daily Post ta rawaito.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar Jigawa Alhaji Bala Ibrahim.
KARANTA WANNAN: NEMA Ta Karbi ‘Yan Najeriya 109 Da Suka Dawo Daga Kasar Libya
Sauran wadanda aka nada sune; Muhammad Salisu Seeker, Mataimaki na Musamman kan harkokin daukar Hoto da Bugawa, Garba Muhammad Hadejia, Mataimaki na Musamman na Sabbin Kafafen Yada Labarai na I.
Sannan akwai Umar Suleiman, Mataimaki na Musamman na Sabbin Kafafen yada labarai na zamani II.
Sanarwar ta ce dukkan nade-naden sun fara aiki nan take.
A wani labarin kuma,An Kuma: Majalisar Dokokin Wata Jiha Ta Dakatar Da Wani Shugaban Karamar Hukuma
Majalisar dokokin Oyo ta dakatar da karin wani shugaban karamar hukumar a jihar.
Da dakatar da shugaban karamar hukumar ya biyo bayan wasu zarge-zarge da ake yi masa.
Ko a watan Mayun daya gabata majalisar dokokin ta dakatar da shugaban karamar hukumar Irepo, Adediran bisa zargin karkatar da kudade.