Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar ya baiwa masu riƙe da Mukaman siyasa a jihar kuma suke son tsayawa takara, umarnin su ajiye Mukaman su.
Mai baiwa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai Habibu Nuhu Kila ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da ya fitar a yau, tare da rabata ga manema labarai.
Kila ya ce Gwamnan ya ce duk wani da aka naɗa a muƙami a jihar yayi murabus daga yau Laraba zuwa Litinin 16 ga watan Mayu na wannan shekara.
Kwamishina yada labarai da bunkasa wasanni da matasa Alhaji Bala Ibrahim ne ya bayar da wannan umarni a madadin Gwamnan, jim kadan da kammala zaman majalisar zartarwar jihar a yau.
Daga nan sai gwamnan yayi musu fatan alkhairi da kuma nasara a abubuwan da suka sanya a gaba.
Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Tuni dai wasu jihohi irin su Kano suka dade da bayar da irin wannan umarni, yayin da har yanzu akwai saura da basu karbi wannan umarnin ba.