By Ishaq Dabai
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong zai yi jawabi kai tsaye ga al’ummar mazauna jihar filato.
Sanarwar wacce Darakta kan harkokin yada labarai da al’amuran jama’a na gwamnan jihar Filato, Dakta Makut Simon Macham ya tabbatar da hakan a yammacin ranar lahadi.
Acewar sanarwar akwanakin nan ana samun cigaba a jihar, wanda hakan yasa gwamnan zaiyi jawabi ga jama’ar jihar agobe litinin 30 gawatan Agusta.
“Muna shawartar mabiyan mu da masu kafar yada labarai ta zamani da gidaje radiyo da gidan talebishi na jiha dasu kuna tashoshin dan saurari jawabin da gwamna zai gabatar da misalin karfe 6:30 nasafe.
Baya da haka asauran wurare babu tabbacin wani labari da yake faruwa akewayen bayan da akasa dokar hana zirga zirga ta sa’oi 24 a karamar hukumar Jos ta Arewa da yiwuwar a dage dokar.