By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya mika sakon ta’aziyyarsa ga shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, bisa rasuwar dan uwansa, Sani Dangote, wanda shi ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote.
“Mun samu labarin rasuwar wannan mai martaba Alhaji Sani Dangote cikin kaduwa da jimami, Jihar Kano, kasarmu Najeriya da ’yan kasuwa sun yi hasara hazikin dan adam,” in ji shi.
Gwamnan ya koka da cewa mutuwar sa ba wai kawai ta tayar da hankali ga iyalan mamacin ba “harma ga daukacin al’ummar Kano, musamman ‘yan jihar Kano. Mun yi hasarar wani abu mai daraja a cikin ’yan kasuwa.
“Don haka a madadin gwamnatin jihar Kano, ni gwamnan jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Alhaji Sani Dangote, da dan uwansa, Alhaji Aliko Dangote, bisa rasuwarsa kanin sa” a cewar Ganduje.
Kazalika ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan mamacin da rahma yasa aljanna ce makomarsa ya kuma yiwa iyalansa fatan samun kwarin giwwa wajen jure rashin da ba za a iya kwatantawa ba.