Gwamnan Jihar Nassarawa Abdullahi Sule ya kori sakataren gwamnatin Aliyu Ahmed Tijjani daga aiki ranar Litinin.
Hakan ya fito ne daga wata sanarwa da hadimin gwamnan ya sanya hannu Hamza Gayam, ya umarci sakataren gwamnatin da ya dawo da dukkanin wani abu da yasan mallakin gwamnatin ne daka karkashin ikonsa.
Sai dai ya zuwa yanzu babu wanu dalili da za a iya cewa shi ne sanadin sallamar sakataren daga aiki, duk da sulhu da majalisar jihar da ta yi tsakanin gwamnan da sakataren kan badakalar aikin makarantu wanda kudaden ya kai Miliyan 284.5.