By Abbas Yakubu Yaura
Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya sayi fom din tsayawa takara a jam’iyyar APC domin neman kujerar Sanatan Neja ta Arewa a zaben 2023.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kungiyar kwamishinoni masu yiwa kasa hidima ne suka sayi fom din a madadinsa.
A wata wasika da kansa daya sanyawa hannu, Bello ya ce sha’awarsa ta tsayawa takarar majalisar dattawa kira ne da jama’arsa suka yi masa wanda ya ce suna ganinsa a matsayin jakadan da ya cancanta ya wakilce su.
Yayin karbar fom din tsayawa takara daga kwamishinonin sa, Bello ya yi kira da a yi gaskiya da adalci a zaben 2023.
“Duk da cewa ban so tsayawa takarar majalisar dattawa bayan na shafe shekaru 8 ina mulki a matsayina na Gwamna, amma sai da na yi biyayya ga burinku da daman ku da kuka shiga da gaske.” Inji shi.
Ya kara da cewa irin goyon bayan da ya samu ya cika shi da nuna sha’awar tsayawa takara, inda ya kara da cewa kwarin gwiwa da hadin kai da sauran masu neman shiyyar da kuma jam’iyyun siyasa ke nunawa, wanda a cewarsa ya fifita muradun shiyyar sama da nasu son ren
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro Gwamna Bello ya bayyana cewa daya daga cikin jiga-jigan ‘yan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar, Umar Nasko, ya sauka ne domin nuna goyon bayansa ga burinsa.
Gwamnan ya ce wani fitaccen dan takara, Sani Duba shi ma ya janye burinsa, ya kara da cewa, “Na yaba musu da abin da suka yi.”