
Gwamnan jihar neja ya kaddamar da Kungiyar ‘Yan sakai don wanzar da tsaro.
Gwamnan jihar neja Abubakar Sani Bello Lolo ya kaddamar da ‘yan sakan domin kula da rayukan al’ummar dake jihar.
Jaridar TVCNews ta wallafa Gwamnan ya bayyanawa iyayen yaranda aka sace a makarantar Tanko Salihu Islamiyya dake garin Tegina nanda lokaci kadan yaransu zasu dawo gida cikin koshin Lafiya.
KARANTA WANNAN:-
Haryanzu nine Jagora na jam’iyar APGA Inji Victor Oye
Wannan kungiyar ‘yan sakan matasa ne na musamman da zasuyi matukar kokarin wajan tabbatarda tsaro a garin Tegina da sauran kananan hukumomin dake jihar.
Motoci goma da mashina ashirin gami da zaratan matasa dari da sittin da daya ne aka kaddamar a matsayin kaso na farko a yunkurin kawo karshen ta’adanci a yankin.
‘Yan kungiyar sakan an debosu ne cikin manya manyan kungiyoyin sakan dake cikin kananan hukumomi tara daga cikin 24, an kaddamar dasu ne a babban ofishin ‘yan sanda dake garin Minna babban birnin jihar.
Gwamnan yayi matukar farin ciki ganin irin yadda matasan suka sadaukar da rayuwarsu wajan kawo karshen ta’adanci, sannan yace daga cikin aikinsu kula da kungiyoyin matasa marasa kunya dake cikin garin Minna, sannan yayi alkawarin bayarda gudun mawarsa domin ganin aikin ya tafi dai-dai.
A WANI LABARIN:- Haryanzu nine Jagora na jam’iyar APGA Inji Victor Oye.
Shugaban Jam’iyyar APGA Victor Oye ya ce batun dakatar da shi da wasu jami’an jam’iyyar ke yi wannan kanzon kurege ne”
Jaridar TVCNEWS ta ruwaito Oye ya bayyana hakan ne lokacinda ake fira dashi ta wayar tarho Awka ranar talata.
Jaridar Vanguard ta wallafa. Yace hakan yazama ruwan dare duk lokacin da aka ga zabe ya karato sai a dinga yada labarai don karkatar da hankulan mutane