lolo

Gwamnan Jihar Neja Ya Rushe Mukarraban Gwammati

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello a jiya Litinin da daddare ya rushe mukarraban gwamnatin jihar inda ya bukace su, da su mika rahoton harkokin ma’aikatar su ga sakatarorin ma’aikatun jihar tare da sauran wadanda ke rike da mukaman hukumomi su mika rahoton ayyukansu ga manyan ma’aikatan gwamnatin jihar.

Sakataren watsa labarai na gwamnan Malam Jibrin Ndache, ne ya sanar da hakan bayan wani taro da suka yi da mukarraban gwamnatin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *