Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya umarci kwalejin tsaro ta kasa (National Defence College Course 30) da ta samar da dabarun tsaro da zai kawo karshen rashin tsaro a jihar.
Da yake gabatar da laccar sa mai suna Dabarun yin shugabanci da turanci Strategic leadership: gogewar siyasa ta. Gwamna Sani Bello ya ce lokacin da gwamnatinsa ta hau mulki a shekarar 2015 sun dauki salon shugabancin siyasa wanda ya shafi mutane.
Ya ce an nuna hakan a cikin tsarin kasafin kudin da suka dauka a cikin kasafin kudin 2018.
Ya ce sun zagaya al’umma domin su tambayi jama’a abin da suke so ba su dauka a madadinsu ba tare da lura da cewa al’ummomi daban-daban suna da sha’awarsu ta musamman .
Ya lura cewa a matsayinsa na shugaba mai dabaru mutane ba za su taba gamsuwa da kokarin shugaban ba amma dole ne shugaba ya tabbatar da cewa an samu sakamako na gaske kuma mabiya za su lura.
Wannan abin takaici ne matuka yadda shugabannin siyasa ke kallon shugabanci a matsayin wata hanya ta cimma muradun kashin kai.
Da yake magana game da rashin tsaro a jihar, ya ce a wasu lokutan jami’an tsaro suna samun sa’o’i 24 na bayanan motsin ‘yan bindiga da inda suke tunkarar su kafin a kai musu hari amma sai a makara.
Ya kuma kara da cewa, ‘yan bindiga a jihar sun fara gudanar da ayyukansu tun daga fashi da makami zuwa satar shanu, kuma a yanzu zuwa garkuwa da mutane dole ne hukumomin tsaro da ke kula da iyakokin su koma su kara kaimi wajen aikin sintiri a kan iyakokin kasar domin lura da kwararowar mutanen da ke shigowa kasar.
Ya ce jihar Neja na aiwatar da cikakken cin gashin kan kananan hukumomi kuma ba ta shiga asusunsu.
Sai dai ya damu da yadda shugabanci a matakin kananan hukumomi ya canza kuma baya tunanin cewa gwamnonin su shiga tsakani don kada manufar wannan hukuma ta ka sa.