Gwamnan Jihar Ogun Abiodun yakai ziyara shagunan da wuta ta kone
Jaridar tvcnewstvcnews ta ruwaito cewa Dapo Abiodun Gwamnan Ogun yakai ziyara a kantin Opic inda wuta ba babbaka shagunan, lokacin ziyarar ya bayyana rashin jindadinsa saboda aukuwar lamarin.
KARANTA:- Gwamna Elrufai ya sallami maaikata 99 ya Kuma bayyana cewa zai cigaba
Sannan Gwamnan ya aikada sakon ban hakuri ga iyalan da abun ya rutsa dasu. Hakazalika ya yabama mayukuntan kota kwana kan irin bajintar da sukayi na daukan matakin hana wutar yin babban ta’azi.
Sannan ya Gwamnan ya yaba wa gwamnatin Legas gami da nuna bacin ransa akan musabbabin aukuwar lamarin.
Gwanman ya bayyana cewar gwamnatin Ogun zata hada kai da gwamnatin Legas wajan dakile aukuwar irin wannan abun.
A WANI LABARIN:- Kamfanin MTN sun ce da akwai samun karancin sabis saboda tashin hankalin dake faruwa a kasar nan.
Kamfanin ya bayyana cewar da yiwuwar samun karancin sabis duba da irin rikice-rikicen dake tashi a ko wane yanki dake fadin kasar nan.
Wannan shi zai kawo cikas lokacinda zamu aika masu gyara don cigaban sabis din.
Nigeria tana yin bakin kokarinta wajan fada kungiyar Boko Haram tun bayan sama da shekaru masu yawa, gami da satar mutane don biyan kudin fansa, yin awon gaba da dalibai da kuma tafiya da shanun a yankin kudu maso gabas na kasar najeriya.
A gabas maso arewan dake ƙasar, sannan da jihohin Najeriya ta tsakiya farmakin yan ta’addan ya janyo asarar rayukan mutane wanda ba a san adadinsu ba da miliyoyin kudade.