Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya kamu da cutar Korona, biyo bayan gwajin cutar da aka masa .
Gwamna Akeredolu a cikin wani bidiyo, ya ce sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma zai fara killace kansa, domin likitoci su kula da lafiyarsa.
“Sakamon ya fito yau Talata 30 ga watan Yuni, 2020 kuma na kamu da cutar.
https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-gwamnan-jihar-abia-ya-kamu-da-corona/
“Likitocina sun yanke shawarar cewa in fara karbar magani, tare da kuma killace kai na”, inji shi.
Gwamnan wanda ya ce alamar cutar tasa ta fara ne daga jin yanayin zazzabin malaria, sannan gwamnan ya shawarci masu jin alamu irin na malariya a jihar da su je a yi musu gwaji.
Ya kuma bukaci jami’ai da mukarraban gwamnatinsa da su ci gaba da gudanar da ayyuka yadda suka saba, yana mai cewa shi ma zai ci gaba da gudanar da aikin ofishina daga killace.