Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya nada dansa Babajide a matsayin Darakta-Janar na sashin lura da ayyuka da aiwatar da ayyuka a (PPIMU).
Akeredolu ya sanar da nadin dansa tare da nadin kwamishinoni 14. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Donald Ojogo, ya fitar a ranar Talata.
“Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN, ya nada sabbin kwamishinoni 14 da kuma masu ba da shawara na musamman guda bakwai,” in ji sanarwar.
“ kwamishinonin da aka nada sune kamar haka: Mrs Bamidele Ademola Olateju (Akoko South East), Otunba Adefarati Gboyega (Akoko South West), Rt Hon Olotu Fatai (Akoko North East), Dr. Julianah Oshadahun (Akoko North West), Otunba Dele Ologun. (Akure North), Mr. Sunday Adekunle (Idanre) da Engr. Razaq Obe (Ifedore).
“Sauran su hadar da Dr. Banji Awolowo Ajaka (Ilaje), Fasto Emmanuel Igbasan (Irele), Mrs Yetunde Adeyanju (Odigbo), Mista Femi Agagu (Okitipupa), Hon. Akinlosotu (Ondo East), Hon Omolola Fagbemi (Ondo West) da Cif Olayato Aribo (Ose).
“Wadanda aka zaba a matsayin masu ba da shawara na musamman sun hada da: Cif (Dr) Victor Ategbole, Dr. (Mrs) Wunmi Egbayelo Ilawole, Hon. (Barr) Tobi Ogunleye Felix, Dr. Ajibayo Adeyeye, Mrs Olamide Falana, Dr. Francis Adedayo Faduyile da Mr Oyeniyi Oseni.
“Za a mika sunayen wadanda aka nada, musamman mukamin kwamishina zuwa majalisar dokoki domin tantancewa, “Duk wadanda aka zaba/ za a rantsar da su a ranar da za a sanar da su daga baya, bayan bin matakan tantancewa a majalisa. Gwamna yana yi wa duk wadanda aka zaba fatan alheri.”