Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bai wa daya daga cikin wadanda rikicin ‘yan sanda ya rutsa da su, Samuel Ogundeji tallafin karatu a wani bangare na shawarwarin ENDSARS da aka mika masa.
Rahoton wanda shugaban kwamitin, Mai shari’a Badejoko Adeniji ya mika masa, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati a zauren majalisar zartarwa na ofishin gwamna da ke Ibadan.
Gwamnan a jawabinsa ya bada tabbacin aiwatar da rahoton cikin gaggawa domin samun isassun kudade.
Gwamna Makinde ya ce zai bayar da tallafin karatu ga matashin mai shekaru 23 da aka zarge shi da laifin satar jakar banki tare da cin zarafin wasu jami’an SARS da suka mutu wanda daga baya ya makance.
A nasa jawabin shugaban kwamitin, Mai shari’a Badejoko Adeniji, ya bayyana cewa an samu koke-koke 151 amma an saurari koke-koke 121 har zuwa karshe yayin da aka soke koke 30 saboda wasu hujjoji da ba a tantance ba.
Idan za a iya tunawa, a watan Oktoban shekarar 2020 ne matasan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyukan rashin dacewa na SARS wanda hakan ya sa gwamnatocin jihohi suka kafa kwamitin bincike.