Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya yabawa jami’an tsaro a jiharsa kan yadda suka tashi tsaye wajen ganin sun dakile yunkurin masu garkuwa da mutane na sanya ta’addanci a tsakanin jama’a.
A cikin wani sako, Gwamna Lalong ya bayyana jin dadinsa kan yadda jami’an tsaro suka yi gaggawar amsa kiran da ake yi na sace-sacen mutane, wanda ya yi sanadin wargaza ayyukan bata gari, inda aka ceto wasu da abin ya shafa tare da kama wadanda ake zargi.
An ceto Gwom Rwey na gundumar Vwang, Da Gyang Gutt Balak, nan da nan bayan da aka yi garkuwa da su, da kuma kame wasu da ake zargi, a cewar Lalong, mataki ne mai kyau da ya kamata a dore.
Ya bayar da misali da irin wannan lamari inda aka kubutar da wasu dalibai uku na jihar Filato jim kadan bayan sace su daga makarantar da ke Heipang.
Gwamna Lalong ya karfafa gwiwar hukumomin tsaro kamar ‘yan sanda, DSS, Operation Safe Haven, Operation Rainbow, NSCDC, sauran jami’an soji, da kungiyoyin ‘yan banga da su cigaba da matsa lamba kan masu aikata laifuka, yana mai alkawarin cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa don taimaka musu wajen fatattakar masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a jihar.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen sanya hannu kan takardar hukuncin kisa ga duk wani mai garkuwa da mutane da aka samu da laifin aikata laifin kamar yadda dokar hana garkuwa da mutane da aka rattabawa hannu a bara ta tanadi hukuncin kisa wanda a shirye yake a aiwatar da shi.
Lalong ya kuma bukaci mazauna jihar Filato da su baiwa hukumomin tsaro bayanan sirri, tare da basu damar mayar da martani, har ma da hasashen ayyukan miyagu da ke kokarin lalata zaman lafiyar jihar.