Biyo bayan yawaitar aikace-aikacen ƴan ta’adda, da masu garkuwa da mutane ga al’ummomi, Gwamnatin jahar Kaduna ta ɓullo da wasu sabbin Dokoki domin yaƙi da ƴan bindiga daɗi.
Kwamishinan tsaron cikin gida na Jahar Samuel Aruwan ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa Manema Labarai jawabi a ranar Laraba, game da sabbin dokokin da jahar ta ɓullo dasu domin yaƙi da ƴan ta’adda.
Kwamishinan yace biyo bayan taro da akayi da jami’an tsaro domin fatattakar ƴan ta’adda a maɓoyar su, gwamnatin jahar ta amince da ɗaukar tsauraran matakai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rashin Tsaro: A daina kashe kashe, Fafaroma Francis Ya Fadawa Buhari
Kwamishinan ya bayyana cewa, daga ranar Alhamis 30 ga watan Satumba na Shekarar 2021, an hana amfani da mashina na hayaz ko na gida na tsawon watanni uku, gami da takaitar zirga-zirgar ƴan ƙurƙura, a yayinda aka amince da su riƙa aiki kaɗai daga karfe 6 na safe zuwa ƙarfe 7 na yamma.
Kwamishinan ya ƙara dacewa, dukkanin ƴan ƙurƙurar zasu cire tamfal ɗin su, a dukkanin lokacin da doka ta yarje masu gudanar da harkokin su a faɗin jahar.
Dukkanin ababen hawa da ake haya dasu dole suyi fentin ruwan ɗorowa da baƙi a cikin kwanaki 30.
Gwamnatin ta kuma hana riƙewa ko waldar duk wani makami mai haɗari, gami da hana saida man fetur a jarka, ko wani wurin zubawa a ƙananan hukumomin Birnin Gwari, da Giwa, da Chikun, da Igabi da Kachia da kuma Kagarko gami da ƙaramar hukumar Kajuru.
Acewar Samuel Aruwan, Gwamnati ta kuma hana saida ɗaukar gawayi zuwa wani wuri, da hana ɗaukar dabbobi zuwa wajen jahar.
Ya kuma ƙara dacewa, Dokar ta kuma haramta kasuwannin mako a ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa da suka haɗa da Birnin Gwari, da Giwa, da Chikun da Igabi sa Kajuru gami da kasuwar kawo ta Kaduna ta Arewa.
“Gwamnatin Jahar Kaduna na bada haƙuri akan rashin jindadi da dokokin zasu haifar, wanda keda manufar samar da zaman lafiya. Gwamnati na kira ga dukkanin magidanta dasu zama masu fahimta da bayar da haɗin kai ga dokar, a wannan lokaci na matsatsi.” Inji shi.
Yace an ɗauki matakan ne domin tallafawa ƙoƙarin jami’an tsaro na yaƙi da ta’addanci a jahar, wanda a cewar sa ƴan ta’adda sunyi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, da kuma karɓar kuɗaɗen fansa a hannun jama’a.
Aruwan ya bada tabbacin cewa, gwamnati zata maido da layukan sadarwa a duk lokacin da aka samu aka samu nasarar murƙushe ƴan ta’adda a faɗin jahar.