Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a yau Juma’a ya halarci addu’a ta musamman da aka gudanar domin tunawa da cikar Alh. Aminu Ado Bayero shekaru 2 a matsayin Sarkin Kano.
Taron Sallah na Musamman wanda aka gudanar a Babban Masallacin Juma’a na Kano ya samu jagoranci Babban Limamin Kano, Farfesa Muhammad Sani Zahraddeen da Wazirin Kano Alhaji Sa’ad Shehu Gidado.
A addu’o’in da suka yi na daban, sun yi wa’azin ‘yan’uwantaka da hadin kai tare da addu’a ga Allah Madaukakin Sarki da ya ci gaba da zaunar da Kano Lafiya a tsakanin al’ummar Kano da kasa baki daya.
Sun kuma yi godiya ga Allah da ya sanya sarautar Alh. Aminu Ado Bayero ta zama shaida ga dimbin ci gaban masarautar Kano da ma jihar baki daya.
A nasa bangaren, Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Bayero ya yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba shi damar yi wa al’ummarsa hidima.
Hakazalika ya yaba da goyon bayan da gwamnatin jiha da ‘yan majalisar masarautu da al’ummar jihar suka ba shi a cikin shekaru 2 da suka gabata.
Sarkin ya kuma yi kira ga ‘yan kasuwa da kada su kara tsadar kayan masarufi yayin da azumin watan Ramadan ke gabatowa.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya taya Sarkin murnar nasarar da aka samu a cikin wannan lokaci.
Ya kuma bukaci Sarkin da ya ci gaba da bayar da goyon bayansa wajen ganin an samu hadin kai da zaman lafiya da tsaron al’ummar Masarautarsa da kasa baki daya.
Taron Sallar ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da ‘yan majalisar masarautu da malaman addinin Islama da sauran masu ruwa da tsaki.
Comments 1